Saudiyya za ta kori mutane miliyan 1.2 wadanda ba ‘yan kasar ba a cikin wannan shekarar

0
1594

A wata kididdiga da kamfanin Jadwa na kasar Saudiyya ya fitar, kimanin mutane miliyan daya da dubu dari biyu ne za su bar kasar saudiyya zuwa kasashen su daga nan zuwa karshen wannan shekarar.

Duk da wannan korar mutane wadanda ba ‘yan kasar ba da Saudiyyar za ta yi, matsalar rashin aikin yi za ta cigaba da zama a kashi 12 cikin dari daga nan zuwa karshen wannan shekarar.

A rahoton da kamfanin na Jadwa ya fitar, ma’aikatun da wannan lamari zai shafa sun hada da asibitoci, wuraren sayar da abinci, kamfanonin tafiye-tafiye, kamfanonin tsaro, da kuma kamfanoni na gine-gine.

Duk da cewa an kasar na kokarin cire dokar hana zirga-zirga, amma wasu wuraren za su dauki lokaci kafin su cigaba da aiki, irinsu otel-otel, kamfanonin sufuri, wuraren sayar da abinci, wuraren shakatawa, da kuma wuraren nishadi.

Haka rahoton ya bayyana cewa hukumomin kasar sun sanar da cewa ‘yan kasar za su cigaba da rike ayyukansu kamar yadda suka saba, inda ya zuwa yanzu kasar ta Saudiyya ta biya kimanin Riyal biliyan 2.4 ga marasa karfi a kasar domin tallafa musu a wannan lokaci.

Da wannan yawan mutane da ake shirin kora a kasar, akwai dama sosai ga mutanen kasar wajen samun ayyukan yi. Yayin da gwamnatin kasar ta dakatar da bawa mutane Visa.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here