Sarkin Musulmai ya nuna bacin ransa akan gwamnonin da zasu bari ayi sallar idi a jihohinsu

1
366

An samu bambancin ra’ayi tsakanin Sarkin Musulmi da wasu gwamnoni a jihohin arewacin Najeriya akan sallar idi da za a gabatar a karshen makon nan.

Sarkin Musulmai Sa’ad Abubakar III, wanda yake shine shugaban kwamitin koli ta addinin Musulunci a Najeriya, ya bayar da umarnin Musulmai su gabatar da sallar idi a cikin gidajensu a matsayin yunkuri na dakile yaduwar cutar a cikin al’umma.

Sai dai wasu gwamnonin sun cire dokar hana fita a jihohinsu, inda suka bar Musulmai su gabatar da salla a cikin jam’i.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a farkon makon nan ya bayyana kudurinshi na kyale mutane su gabatar da sallar Juma’a a gobe, sannan kuma su gabatar da sallar idi a ranar sallah.

Haka a ranar Laraba, gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya bayyana cewa shi ma zai bari a gabatar da sallar idi a jihar da sharadin zasu bi dokar nisantar juna tare da sanya takunkumi.

Haka sauran jihohi irinsu, Yobe, Jigawa, Borno da Zamfara duka sun bude Masallatai don cigaba da gabatar da sallah.

A sanarwar da sakatare janar na kungiyar NSCIA, Farfesa Salisu Shehu ya fitar a ranar Laraba, ya ce: “a yayin da watan Ramadana yake karatowa, karamar sallah na zuwa, yana da matukar muhimmanci mu san cewa yanzu lokaci ne da muke cikin wani hali, da abubuwan da muka saba yi a baya baza su yiwu ba yanzu.

“Saboda haka muna sanar da jama’a su san cewa sallar idi ba dole bace a addinin Musulunci, kuma babu amfani idan har yinta zai sabawa shari’a, tsaro, lafiya, da sauransu.

“Musulmai su gabatar da sallar idi sannan kuma su dauki kwakkwaran mataki wajen kula da lafiyarsu.

“Muna bayar da shawara da kada a gabatar da sallar a filin idi, a gabatar da ita a Masallatai domin gujewa taruwa da ta wuce misali.

“Haka kuma a jihohin da basu bawa mutane damar gabatar da sallar a jam’i ba, muna rokon al’umma su bi doka kamar yadda aka sanyata.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here