Sarakunan gargajiya ne suke taimakawa ‘yan bindiga a Katsina – Fadar shugaban kasa

1
949

Wasu daga cikin sarakunan gargajiya ne suke taimakawa ‘yan bindiga a jihar Katsina, cewar mai taimakawa shugaban kasa, Malam Garba Shehu.

Da yake hira da Channels Television a yau Litinin dinnan, Garba Shehu ya ce sarakunan gargajiyan sune suke taimakawa ‘yan bindigar suke guduwa idan jami’an tsaro suka kai musu hari.

‘Yan bindigar dai sun shafe mako guda kenan suna kai wa al’umma hari a kauyuka, inda suka kashe kimanin mutane 100.

“Ba wai muna zargin wani bane kai tsaye, amma gaskiya ne hatta a cikin garin shugaban kasar, akwai sarakunan gargajiya da aka kama suna hada kai da ‘yan bindiga suna cutar da mutanensu,” ya ce.

“A jihohin Zamfara, akwai sarakuna da masu gari da yawa da aka kore su daga fadarsu.

“Abin shine akwai masu cin riba a kowanne irin abu da yake faruwa.

“Hakan ya sanya rundunar sojin Najeriya ta ajiye jiragen sama a jihar ta Katsina, har yanzu suna can a ajiye.

“A farkon fara hare-haren su a Zamfara, inda a lokacin shine mafakarsu, sun fahimci cewa da zarar jirgin yaki ya tashi daga Katsina kafin ya isa Zamfara za a iya kiran waya kuma wadanda za a kai harin kansu za su gudu.

“A karshe ya sanya dole ake tashin jiragen yaki daga jihohin Kaduna da Kano idan za a kaiwa ‘yan bindigar hari a Zamfara.

Garba Shehu ya roki kowa ya taimaka wajen kawo karshen wannan abu ta hanyar bayar da rahoton abubuwan da ‘yan bindigar suke yi.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here