Sani Khalid: Gurgu marar kafa da ya kammala digiri a Jami’ar ABU da sakamako mafi daraja

0
303

A tsakiyar shekarar 2019 ne lokacin da wani matashin saurayi ya jawo hankulan mutane da dama a shafukan sadarwa, bayan wani ya wallafa labarin nasarar da ya samu duk kuwa da matsalar da yake fama da ita ta larura.

Wani mai suna Mahmoud Shu’aibu shine ya wallafa wannan gagarumar nasara da wannan mutumi ya samu a shafin Twitter, inda ya bayyana nasarar da saurayin mai suna Sani Khalid ya samu a jami’a.

A cewar Shu’aibu, mutumin wanda bashi da kafa ya kammala digirin shi da sakamako mafi daraja a bangaren kimiyya ta halitta wato (Biological Science) a turance a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria.

“Sani Khalid kenan daga jihar Katsina, wanda ya kammala karatu a fannin kimiyyar halittu, a jami’ar Ahmadu Bello Zaria, inda ya fita da maki CGPA 4.56 (sakamako mafi daraja) duk kuwa da cewa gurgune bashi da kafa.”

Wannan rubutu da Shu’aib ya wallafa mutane sunyi ta magana a kanshi, inda kowa ya dinga sanya albarka yana fadar albarkacin bakinsa.

Wannan dai na nuni da cewa dan Allah yayi mutum da matsala kowacce iri ce hakan ba yana nufin ba zai iya yin abinda wasu ke yi ba.

Maimakon Sani Khalid ya fara bin hanya da gidaje yana yin bara, ya gane cewa makaranta ita ce hasken rayuwa, wannan larura tasa bata saka ya hakura da cimma burinshi ba. Muna fatan Allah ya yiwa rayuwar shi albarka, ya kuma saka masu larura irin tashi dama wadanda ba irin tashi ba su gane muhimmancin neman na kai da karatu.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here