Sanata Ali Ndume ya bukaci gwamnatin tarayya ta rage albashin ma’aikata

0
1144

Sanata Ali Ndume yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta rage albashin ma’aikatan Najeriya da suke zaune a gida basa aiki saboda annobar coronavirus da ta hana zirga-zirga.

Ndume wanda yake shine shugaban kwamitin sanatoci ta sojojin Najeriya, ya bayar da wannan shawara ne a lokacin da yake magana da manema labarai a Maiduguri, babban birnin jihar Borno a jiya Litinin 8 ga watan Yuni.

Ya ce duk da fama da ake da annobar COVID-19 a Najeriya, gwamnatin tarayya tana kashe makudan kudade akan abubuwa na yau da kullum. Ya ce mutanen da basu zuwa aiki saboda wannan annoba a dinga basu tallafi, amma kuma a rage albashinsu.

“Ya kamata gwamnati tayi duba akan kudaden da take kashewa akan ma’aikata wanda yake cinye kimanin kashi 70 na kasafin kudi. Ya kamata a ware wasu daga ciki a sanya jari. Mutane su sadaukar da wani bangare na albashin su. Wannan shine lokaci da za a duba al’amura sosai.

“Ina ganin ya kamata a samu mutane su sadaukar da wani bangare na albashinsu, musamman ma’aikata. Yawancin mutane basa zuwa wuraren aiki saboda cutar coronavirus da ta hana fita, kuma ana biyansu albashi daidai. Shin akwai wata hujja akan hana?

“Idan har mutane baza su fita wajen aiki ba saboda cutar coronavirus, ina ganin kamata yayi a rage musu albashi, sannan a dinga basu kayan tallafi.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here