- Elizabeth Owusua, kyakkyawar budurwa ‘yar kasar Ghana da ta cimma burinta na rayuwa ta zama lauya sannnan kuma ma’aikaciyar lafiya a lokaci daya
- Mafarkinta ya fara zama gaskiya tun a shekarar 2005 da ta samu gurbin karatu a fannin lafiya
- A shekarar 2019, kyakkyawar budurwar mai ilimi an dauke ta aikin lauya bayan kammala karatu a fannin shari’a
Kyakkyawar budurwa ‘yar kasar Ghana mai suna Elizabeth Owusua, ta cimma burin da ta dauka tun tana yarinya karama, inda ta zama ma’aikaciyar lafiya da kuma lauya duka a lokaci daya.
A hirar da budurwar tayi da jaridar yen.com.ng, ta bayyana cewa tun tana yarinya karama tana da mafarkin ta zama lauya, sannan kuma tayi aiki a bangaren lafiya a lokaci daya.
A cewar Elizabeth duk da yake ta bata lokaci kafin ta cimma mafarkinta, amma bata taba tunanin cewa mafarkinta zai zama gaskiya ba.
Kyakkyawar budurwar ta ce: “Naje makarantar koyon aikin lafiya ta Korle Bu, inda na kammala karatun difloma a can a shekarar 2008, na fara aiki a matsayin ma’aikaciyar a shekarar 2010, bayan na bautawa kasa ta.”
Daga nan, Owusua ta cigaba da cewa ta cigaba da karatu a Central University College, inda ta kammala digiri a fannin lafiya a shekarar 2013.
A shekarar 2014, Owusua ta fara karatu a fannin shari’a, inda take zuwa makarantar da rana ta kuma je asibiti aiki da dare, bayan kammala karatun ta a fannin shari’a ta samu aikin lauya a shekarar 2019.