Samari sun yiwa ‘yar bautar kasa fyade yayin da taje yin cajin waya a gidansu

0
645

Wasu samari guda biyu masu suna Ofonime Essien da Frank Okon, sun yiwa wata ‘yar bautar kasa wacce aka boye sunanta fyade, a lokacin da taje gidansu yin cajin waya a garin Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom.

Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom sun bayyana cewa tuni sun cafke wadanda ake zargin.

Haka kuma rundunar ta kara da cewa ta sake kama wasu mutane uku da laifin yiwa yara kanana fyade, ciki kuwa hadda wani mai shekaru 55 da ya yiwa ‘yar gidan matarshi fyade.

A wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar CSP N-Nudam Fredrick wacce ya fitar a ranar Talata a Uyo, ya ce mutumin mai shekaru 55 mai suna Udo Ekong Esau, ya yiwa ‘yar gidan matar tashi mai shekaru 15 a duniya fyade.

Ya ce Esau, wanda yake dan kauyen Odot dake karamar hukumar Nsit Atai, ya kori ‘yar gidan matar tashi daga gidansa a lokacin da ya gano cewa tana dauke da ciki.

Haka kuma rundunar ‘yan sandan ta kara da cewa wani dan kungiyar asiri mai suna Ekemini Asuquo ya bayyana cewa ya yaudari wata yarinya mai shekaru 14 ya bata naira 1,500 ya jawo ta zuwa wani otel yayi lalata da ita.

Daga baya kuma Asuquo ya kwace kudin daga wajen yarinyar, ya kuma yi barazanar kasheta idan har ta sanarwa da ‘yan sanda.

Ya bayyana cewa duka wadanda ake zargin sun amsa laifinsu, kuma za su mika su gaban kotu don ta yanke musu hukunci.

Ya gargadi masu irin wannan halayya da su tuba su daina ko kuma su fuskanci fushin shari’a.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here