Sama da mutum 50,000 sun warke daga cutar Coronavirus a kasar Turkiyya

0
162

Ministan lafiya na kasar Turkiyya, Dr Fahrettin Koca ya sanar da cewa mutanen da suka warke daga cutar Coronavirus a kasar cikin sa’a 24 da suka wuce ya ninka yawan wadanda aka samu da cutar kusan sau uku.

A ranar Juma’a 1 ga watan Mayu, kimanin mutane dubu biyar ne suka warke daga cutar, inda yawansu ya zarta wadanda suka kamu da cutar sau 2.25.

A ranar ta Juma’ar lokacin da mutane dubu 4,922 suka warke daga cutar, mutum 2,188 ne kacal cutar ta harba a ranar.

Ya zuwa yanzu dai a kasar ta Turkiyya an yiwa mutane sama da miliyan daya gwajin kwayar cutar ta Coronavirus, inda daga cikinsu aka samu mutum 122,392 da suke dauke da cutar, mutane 53,808 sun warke daga cutar, inda mutum 3,258 suka mutu sanadiyyar cutar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here