Sai karbar kudaden jama’a basa bawa mutane wuta, lokaci yayi da zamu karbo NEPA daga wajen ‘yan kasuwa – Shugaban majalisar dattawa

2
693

A jiya Talata ne shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya bukaci gwamnatin tarayya da tayi duba akan karbo kamfanin wutar lantarki daga hannun ‘yan kasuwa.

Wannan dai na zuwa ne a lokacin da majalisar dattawan ta bukaci gwamnati ta dakatar da kokarin da kamfanin yake na kara kudin wutar lantarki daga ranar 1 ga watan Yuli, duk da fama da wahalar Coronavirus da ake yi a wannan lokacin.

A bayanin da Lawan yayi dangane da wannan lamari, ya ce, idan har Najeriya ta cigaba da zama a haka nan da shekara goma, to dakyar wutar da ake samu a yanzu za a cigaba da samunta nan gaba.

Ahmad Lawan yace duk da makudan kudaden da gwamnatin tarayya take kashewa a fannin wutar lantarkin, amma har yanzu babu wani cigaba da ake samu.

Ya ce: “Mun basu kamfanin wutar lantarkin, amma har yanzu suna zuwa wajen al’umma suna karbar kudade. Ina ganin lokaci yayi da Najeriya za ta karbo kamfanin daga hannunsu. Idan muka cigaba da zama a haka nan da shekara goma baza mu dinga samun wuta ba.

Shugaban majalisar dattawan ya cigaba da cewa, “danka kamfanin wutar lantarki a hannun ‘yan kasuwa bai amfana mana da komai ba, muna tunanin za a samu canji a fannin, amma babu wani abu da ya samu.

“DisCos sun kasa samar mana da wutar lantarki, GenCos suma suna fama da matsaloli. Ina ganin lokaci yayi da zamu daina basu kudaden mu a iska. Ya kamata muyi duba akan wannan lamarin.

“Kwamitin mu za tayi bincike akan tiriliyoyin kudaden da aka kashe. Wannan kudi ne masu tarin yawa. Za mu binciko abinda ya faru. Gwamnati dole tayi duba akan wannan lamari. Ina ganin gwamnati ba ta yin kokarin da ya dace. Muna cikin damuwa saboda babu wutar lantarki, kuma kasar na cikin halin kaka naka yi.

2 COMMENTS

  1. Allah yataimaki seneter Ahmad Lawal, Allah yataimaki majalisar dattawa, Allah yataimaki gwamnatin tarayyar Nigeria data kwato mana hakkinmu a bangaren wutar lantarki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here