Sai dana biya tarar N10,000 da aka kama ni babu takunkumin fuska a Kaduna – Sheikh Yusuf Sambo Rigachikum

0
345

A jiya Asabar ne mataimakin shugaban kungiyar izala na kasa, Sheikh Yusuf Sambo Rigachikum, ya bayyana yadda ya biya tarar naira dubu goma (N10,000) da aka kama shi ya fita babu takunkumin fuska a Kaduna.

Ya ce an kama shi ya karya doka a lokacin da yake cikin mota shi da dan shi guda daya.

Babban Malamin, wanda yake kuma shine shugaban majalisar koli ta shari’a ta jihar Kaduna, ya fada hannun jami’an da gwamnatin jihar Kaduna ta saka akan kama masu karya dokar saka takunkumin fuska.

Ya ce ba halin shi bane fita babu takunkumin fuska, kuma a wannan ranar da lamarin ya faru takunkumin yana cikin motar shi.

“Bana fita ba tare da takunkumin fuska ba, sai a wannan rana da na ajiye shi a cikin mota.

“Na bar gidan rediyon jihar Kaduna, inda nayi hira da manema labarai kafin na wuce gidan abokina dake unguwar Rimi.

“Akan hanyar mu ta dawowa gida, sai ‘yan sanda suka tsayar damu inda suka ci tarar naira dubu biyar ga kowanne daga cikinmu akan bamu saka takunkumin fuska ba.

“Na basu N10,000 ni da dana, kuma na karbi raciti, matar da taci tarar tawa tana kokarin yi mini bayani wai doka ce, nace mata kada ta damu, saboda lokacinsu ne.

“Kamar yadda na fada ba dabi’a ta bace na fita babu takunkumin fuska, saboda nima nayi karatu a bangaren shari’a,” ya ce.

Sheikh Rigachikum ya ce alhakin malaman addini ne su fadakar da mutane su bi doka, amma yace kamata yayi abi doka wajen irin wannan hukuncin, kamata yayi a kai dokar gaban majalisar jiha idan sun amince shikenan sai ta fara aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here