Saboda gajarta ta yasa lokacin da ina saurayi ‘yammata basa kulani – Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai

0
448

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya shiga hira akan wani bidiyo da Teju Babyface ya wallafa a shafin Twitter.

A bidiyon wanda aka dauka a shekarar 2010, inda gwamnan yayi hira da dan wasan barkwancin, El-Rufai ya ce shine sakatare janar na gajerun mutane na Najeriya. Ya kuma bayyana irin kalubalen da ya fuskanta akan rashin tsawon da yake da shi.

“A da ni ne sakatare janar… a lokacin da nake tsakanin shekaru 20 na fuskanci kalubale sosai saboda gajarta ta, saboda kun san lokacin duka kyawawan ‘yammata sun fini tsawo.

“Amma a hankali komai ya zo ya wuce, har na samu kyakkyawar mata mai ilimi na aura, wacce na fita tsawo da kadan.

Da yaci karo da bidiyon a wannan karon, El-Rufai ya tsokani mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, inda ya kirashi da shugaban gajerun mutane na Najeriya na yanzu.

“Na tuna wannan hirar da nayi da Teju Babyface a shekarar 2010…lokaci yana tafiya sosai. Yanzu mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo shine shugaban kungiyar gajerun mutane ta Najeriya.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here