Ronaldo ya zama dan wasan kwallon kafa na 1 a duniya da ya zama biloniya

0
644

Fitaccen dan wasan kwallon kafa, Cristiano Ronaldo ya zama dan wasa na farko a duniya da ya mallaki dala biliyan daya.

A rahoton da Forbes Magazine ta ruwaito, Cristiano Ronaldo ya samu dala miliyan 105 a shekarar da ta gabata, inda ya zama na 4 a cikin taurari guda 100 na duniya da suka fi kudi a shekarar 2020, kuma ya buge abokin hamayyarsa wato Lionel Messi.

“Cristiano Ronaldo ya samu dala miliyan 105 a shekarar da ta gabata, inda ya zama na hudu a cikin taurari dari na duniya da suka fi arziki a shekarar 2020, ya kuma doke abokin hamayyarsa Lionel Messi, inda ya zama dan wasan kwallon kafa na farko a duniya da yake da dala biliyan daya.” Kamar yadda rahoton na Forbes ya nuna.

Post source: Forbes Twitter Page

Dan wasan mai shekaru 35 a duniya, shine tauraro na uku a duniya dake wasa wanda ya kai wannan matsayi, banda Tiger Woods, wanda ya lashe a shekarar 2009, bayan yarjejeniyar da yayi da Nike, sai kuma Floyd Mayweather, wanda ya lashe a shekarar 2017.

Mayweather ya samu yawancin kudinshi a wasan dambe da yake bugawa.

Ronaldo, wanda ya zama na farko da ya kai wannan matsayi a wasan kwallon kafa, ya samu dala miliyan 650 a shekaru 17 da ya kwashe yana wasan kwallon kafa, kuma ana sa ran zai kai dala miliyan 765 daga nan zuwa watan Yunin shekarar 2022, lokacin da kwantiraginsa zai zo karshe.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here