Rikici ya barke yayin da matar aure ta kama mijinta da yayarta wacce suke uwa daya uba daya suna lalata a otel

0
783
Happy couple lying in bed together

Wata mata mai shekaru 27 dake da ‘ya’ya guda uku ta koka a shafukan sadarwa, bayan ta kama mijinta yana lalata da kanwarta da suke uwa daya uba daya.

Da take bayyana yadda lamarin ya faru, ta ce ta kwashe shekara biyu tana samun matsala da mijinta saboda wata mata da yake hira da ita a waya.

Ta ce ta sha samun shi tayi masa magana game da matar, amma sai dai ya bata hakuri ya kuma yi mata alkawarin ba zai kara kula matar ba.

Ta ce har iyayenta ta sanarwa dangane da lamarin, babbar yayarta ta bata shawara akan tayi hakuri tunda dai har yana kula da ita yadda ya kamata.

Kwanan nan sai ta gano cewa mijin nata ya cigaba da kula matar, sai ta yanke shawarar gano abinda yake yi da inda suke haduwa.

Sai ta bishi wani otel da suke haduwa, tana zuwa sai ta ga cewa ashe yayarta ce take kwanciya da mijinta.

Ashe ta sayi sabon layi ne wanda take hira da shi daya kawai, duk cikinmu babu wanda yake da wannan lambar.

Ta ce ta sha kuka har ta gaji, inda ta ce tana tunanin za ta hakura da auren, za ta kyale mijin nata yaje ya auri yayarta.

Ta ce sun jima suna bata hakuri akan kada ta fito da maganar.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka:

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here