Rashin lafiyar jaruma Zulaihat Zeepreety shin da gaske ne asiri aka yi mata?

0
381

Jaruma Zulaihat Ibrahim wacce aka fi sani da Zeepreety tana daya daga cikin jarumai mata na Kannywood da suka shigo masana’antar da kafar dama, duba da yadda tayi kaurin suna cikin lokaci kalilan.

Hakan ya samo asali ne kan yadda jarumar ta kasance mai kwazo da nuna gogewa a harkar ta musamman wajen iya rawa da rausayawa, barkwanci da kuma iya taka kowacce rawa da aka bata a fim.

Sai dai kuma jarumar na fuskantar wani babban kalubale a rayuwar ta wanda takan yi wata rashin lafiya da idan ta fara takan fita hayyacinta ba ta sanin wanda ke kanta har sai an mayar da ita gida tayi jinya, inda wannan karon shine na biyu da irin haka ta faru da jarumar.

Tun farkon shigarta masana’antar jarumar tayi irin wannan rashin lafiya, inda sai da aka mayar da ita gida can Zuru cikin jihar Kebbi tayi jinya.

Tun daga wannan lokacin ne aka fara rade-radin cewa asiri aka yi mata saboda an ga cewa ta fara samun arziki, sai dai kuma masu wannan magana basu da wata hujja kwakkwara.

A ‘yan kwanakin nan dai jarumar ta kara tsintar kanta cikin irin wannan hali na rashin lafiya, inda har matar jarumi Adam A Zango da take kawace a wajenta tayi wani rubutu a shafinta na nuna alhini akan kawartan, wannan rubutu na ta ya tada hankalin masoyan jarumar, saboda kalaman da matar A Zango tayi amfani da su wajen rubutun.

Tun daga wannan lokaci dai ba a kara jin duriyar jarumar ba, kuma ko an kira wayarta ba a samu, sai dai a ‘yan kwanakin nan aka ga ta wallafa wasu hotuna da bidiyo a shafinta na Instagram.

Ganin haka yasa mujallar fim suka tuntubi jarumar domin jin dalilin da yasa kwana biyu aka daina jin duriyar ya, jarumar ta bayyana cewa rashin lafiya tayi wanda yasa sai da ta koma gida jinya, inda a karshe ta bayyana musu cewa ta samu lafiya tana iya yin komai, amma kuma tana gida saboda halin annoba da ake ciki zaman gida ya zama dole da zarar komai ya dawo daidai za ta dawo ta cigaba da harkokinta kamar yadda ta saba.

Wakilin mujallar fim ya tuntube ta domin ya jiyo shin da gaske ne maganar da ake yadawa cewa asiri aka yi mata, inda ta bashi amsa da cewa ta dauka kiranta yayi su gaisa ba neman labari yazo ba, ta ce idan labari yake so za ta kira shi da kanta ta bashi labari idan lokaci yayi.

Har ya zuwa yanzu dai Zulaihat ba ta kira shi ba, kuma bata bayyana gaskiyar lamarin ba, muna fatan Allah ya bara lafiya yasa kaffara ce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here