Rashin ilimi da jahilci sune suka kawo matsalar da ake fama da ita a jihar Kano – Shehu Sani

0
161

Tsohon Sanatan jihar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya alakanta rashin ilimi da kuma bakin jahilci a matsayin abinda ya jawo matsalar da ake fama da ita a jihar Kano.

Tun bayan bullar cutar a jihar a cikin watan Afrilun da ya gabata, mutane na ta faman mutuwa a jihar babu gaira babu dalili.

A ranar Alhamis da Juma’a din nan da suka gabata ne jihar ta samu mutane mafi yawa da suka kamu da cutar a jihar, inda yawan masu cutar ya kai mutum 311 a lokacin.

Da yake mayar da martani akan halin da ake ciki a jihar, tsohon dan majalisar tarayyar ya kuma dora alhakin abinda yake faruwa akan Malaman addini da ‘yan siyasa, ta hanyar nusantar da mutane gaskiyar abinda zai je ya dawo idan cutar ta bulla.

Haka kuma ya cigaba da cewa ko shakka babu rashin ilimi shine babban abinda ya jawo wannan matsala a jihar.

“Rashin ilimi da jahilci shine babban abinda ya sanya aka kasa gano bakin zare kan matsalar Coronavirus a jihar Kano.” A cewar shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here