Rashin ganin darajar mata da ka ke yi yayi yawa – Abike Dabiri ta zargi Isa Ali Pantami da tura ‘yan bindiga ofishinta

0
1065

Shugabar ‘yan Najeriya dake kasashen ketare Abike Dabiri-Erewa, ta mayarwa da ministan sadarwa, Dr Isa Ali Pantami, martani bayan ya karyata zargin da take yi na cewa ya tura mutane da makamai su kori ma’aikatan ta daga ofishin da hukumar NCC ta basu.

A wata hira da tayi da SaharaReporters, Dabiri-Erewa ta zargi ministan da aika ‘yan bindiga da su karbe ofishinta a watan Fabrairu. Sai dai ministan ya karyata wannan zargi da take yi a kanshi ta shafinsa na Twitter, inda ya ce karya take zabga masa.

Tuni dai Abike ta hau shafinta na Twitter ta mayarwa da Pantami martani, inda ta bayyanawa ministan cewa a matsayinshi na malamin addinin Musulunci bai kamata yayi karya ba. A cewar ta rashin ganin darajar mata da yake da shi yayi yawa.

“Bai kamata Malamin addinin Musulunci yayi karya ba, kayi mini haka ne saboda ni mace ce. Rashin ganin darajar mata da kake yi yayi yawa, mu mance da abinda ya faru a watan Fabrairu. Amma ina so ka bayar da duka kayan ofishin mu.” Cewar ta.

Haka kuma ta wallafa wani bidiyo a shafinta na Twitter a safiyar ranar da aka kwace ofishin nasu da sunan ministan ne ya aiko.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here