Rarara ya gwangwaje Aminu Dumbulum da galleliyar mota da naira miliyan 1

0
464

Fitaccen mawakin siyasar nan na Arewacin Najeriya wanda tauraruwarsa take haskawa a yanzu a fannin waka, wato Dauda Kahutu Rarara ya yiwa Aminu Dumbulum goma ta arziki, inda ya gwagwanje shi da sabuwar mota dal da kuma zunzurutun kudi har naira miliyan daya.

A wani bidiyo da Dabo FM ta samu a jiya Juma’a ya nuna yadda fitaccen mawakin ya bayar da kudin da kuma motar mai kirar Honda ga Aminu Dumbulum.

Aminu Dumbulum yana daya daga cikin manyan mawakan jam’iyyar PDP Kwankwasiyya a Kano, amma ya bar jam’iyyar a satin da ya wuce, shine ya rera fitacciyar wakar nan ta Makafin Kwankwaso.

Rarara dai yana daya daga cikin jiga-jigan tafiyar gwamnatin jihar Kano ta gwamnan jihar Dr Abdullahi Umar Ganduje.

A kwanakin bayan ma fitaccen mawakin ya sanya wata gasa ga mawaka, inda ya bukaci suyi waka ga sababbin sarakunan gargajiya da gwamnan jihar ya nada, inda ya ce duk wanda suka lashe gasar zai basu gagarumar kyauta, ta kudi, mota, kujerar hajji, da sauransu.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here