Kowa dai ya san yadda mutane suke yiwa jaruman fina-finan Hausa mata kallon mata marasa daraja, wadanda suka zubar da mutuncinsu.
Fitacciyar jaruma Rahama Sadau tana daya daga cikin matan da ake yiwa wannan kallo, musamman idan aka yi duba da yadda take rayuwarta ta ko in kula, rayuwa ta turawam masu jajayen kunne.
Bayan mutuwar mahaifin jarumi Ali Nuhu mutane da dama sun yi ta yi masa gori akan Babansa ba Musulmi bane, inda shi kuma Young Ustaz da yayi suna a shafukan sadarwa ya fito ya yiwa mutane raddi akan wannan gori da suke masa, a cikin raddin nasa yayi wata gugar zana da ke nuni da cewa da Rahama Sadau yake.
Wannan gugar zana da Young Ustaz yayi bai yiwa jarumar dadi ba, kuma dama ta dade tana hadiye fushinta akan irin wannan kananan maganganu da ake akan irin salon rayuwar da take yi.
Wannan daliline ya sanya tayi wani dogon rubutu a shafinta kan wannan lamarin, inda ta fara da rubuta:
“Yar fim din Hausa ce, saboda haka ku fita harkar ta. Fahimtar al’ummar mu kenan Hausawa cewa ‘yan fim din Hausa musamman ma mata karuwai ne, sannan suna mutunta jaruman kasashen waje har suna daukar su abin koyi.
“Mace a wannan al’ummar da nake zama a cikinta bata da ‘yancin tayi dogaro da kanta ba tare da an jefe ta da zargi ba. Bata kuma da damar yin wani buri da ya wuce kima.
“Ni ce Rahama Sadau kuma ina alfahari da kaina.”
Kana t kara da dogon rubutu akan irin bahaguwar fahimtar da al’umma suke yiwa duk wata mace da asirinta ya rufu, inda ta bukaci mata su kwafi wannan rubutu nata suyi ta yadawa har al’umma su gane.
A cewar ta ita ma daga shafin wata ‘yar uwa ta kwafo sai dai ba mata ba har maza jarumai da abokanan sana’arta sun wallafa wannan rubutu ciki kuwa har da Adam A Zango.
Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka:
Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa
Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com