Raffia Arshad: Ta zama mace ta farko Musulma da aka bawa mukamin Alkali a kasar Ingila

0
1043

Musulma ta zama mace ta farko da aka bawa mukamin alkali dake sanya Hijab a kasar Ingila. Kuma ta na so Musulmai su san cewa za su iya zama duk abinda suka saka a ransu cewa za su zama.

Raffia Arshad, mai shekaru 40 ta fara mafarkin zama alkali tun tana da shekara 11 a duniya, amma kuma a lokacin ba ta da tabbas akan yadda rayuwar za ta kasance mata.

Ta samu nasarar zama lauya, inda daga baya aka ba ta mukamin mataimakiyar alkali a Midlands.

Ta yanke shawarar zama alkali tun tana shekara 11 a duniya (Hoto: Raffia Arshad)

Ta ce: “Na tabbata abu ne mai girma a gare ni, na san wannan ba wai iya ni daya ya shafa ba. Yana da matukar muhimmanci ga sauran mata, ba wai iya matan Musulmai ba, amma a bangare daya yana da matukar muhimmanci ga mata Musulmai. Abin yayi daban a gare ni saboda na shafe shekaru ina so na kawo wannan matsayin, nayi matukar farin ciki lokacin dana ji labari, amma murnar da mutane ke taya ni ita ce tafi bani sha’awa. Na karbi sakonni da yawa daga wajen mutane maza da mata. Amma wanda mata suka turo mini shi yafi taba ni da suka ce, sanya hijabi da suke yi ya saka suna tunanin ko lauya baza a bari su zama ba ballantana mukamin alkali.”

Duk da Raffia tana da kwarewa ta shekara 17 a fannin shari’a, amma duk da haka tana fuskantar kalubale na kyamar addini.

Ta yanke shawarar zama alkali tun tana shekara 11 a duniya (Hoto: Raffia Arshad)

Amma a yayin da nasarar da ta samu ta fito fili, ta ce har yanzu kanta yakan daure akan abokanan aiki a lokacin da za ta shiga dakin shari’a. “Na san nice mace Musulma ta farko da ta samu mukamin alkali. Amma an bani mukamin ne bisa kokarina ba wai saboda ina sanya Hijabi ba.”

Raffia ta nunawa mata Musulmai hanyar da za su bi suyi nasara a fannin shari’a, haka kuma tayi aiki tukuru don inganta daidaito a fannin shari’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here