Pope Francis yayi kira ga duka Kiristocin duniya su gabatar da azumi a watan Ramadana don kawo karshen annobar Coronavirus

0
407

Pope Francis yayi kira ga dukkanin masu imani dasu hada kai su gabatar da azumi a ranar Alhamis don rokar Allah ya kawo dauki kan al’ummar duniya kan annobar coronavirus.

Babbar kungiyar hadin guiwar addinai ta duniya, ta hada gabatar da addu’a a ranar 14 ga watan Mayu, wacce ta fado a cikin watan Ramadana, inda Musulmai suke azumi daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana.

Babban limamin kasar Egypt Ahmad Al-Tayeb, yayi maraba da wannan tsari. Yayi kira ga daukacin al’ummar duniya da su dage da addu’a su kuma dinga bayar da sadaka saboda Allah domin kawo karshen wannan annoba da ta addabi kowacce kasa ta duniya.

Wannan zai zama abu na farko a tarihin duniya, cewar mai taimakawa Pope Francis dake kasar Egypt, Monsignor Yoannis Lahzi Gaid.

“Wannan zai zama karo na farko da dukkanin al’ummar duniya zasu hadu akan abu guda daya suyi addu’a a tare kuma kowanne da yanayin imaninsa, wannan na nuni da cewa imani na hada kan al’umma ba rabawa yake ba,” cewar Gaid a wata hira da yayi da Al Arabiya.

Kwamitin wacce aka kafa ta a shekarar da ta gabata tare da hadin guiwar kasar Dubai na kira ga al’umma da su dage da addu’a akan masana kimiyya domin su samo maganin wannan cuta.

Haka shima Yariman kasar Dubai mai jiran gado, Sheikh Mohammed bin Zayed Al Nahyan, yayi kira ga daukacin al’ummar duniya da su hada kai su gabatar da addu’o’i a ranar 14 ga watan Mayu don neman gafara a wajen Allah ya kawo karshen wannan annobar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here