Paul Bristow: Dan majalisar kasar Birtaniya da yayi alkawarin yin azumin mako 1 don yaji abinda Musulmai suke ji idan sunyi azumi

0
213

Wani dan majalisa a kasar Birtaniya yana azumin mako guda domin ya fuskanci Musulmai da kuma addinin Musulunci da kyau.

Dan majalisar mai suna Paul Bristow, wanda yake dan majalisa ne a Peterborough dake yankin gabashin kasar Ingila, ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na Twitter, inda ya bayyana burinshi na sanin menene watan Ramadana, da kuma sanin abinda Musulmai suke ji idan sunyi azumi.

“Wata Ramadana watane da Musulmai suke kusanta kansu da Ubangiji, sannan kuma su gyara halayensu da kuma dagewa da ibada,” cewar Bristow. “Saboda haka nima haka zanyi azumi a satin farko na watan Ramadana.”

“Ni ba Musulmi bane, amma ina ganin yana da matukar muhimmanci na fuskanci irin abinda Musulmai dubu ashirin da suke a Peterborough suke ji,” cewar Paul.

“Kwarai da gaske azumin da Musulmai suke yi suna bin addininsu ne, ba kuma bin ka’idar bane bama kawai. Sai hakuri da kuma tsari da kuma doka da suke bi shine yafi komai.” Ya bayyana manema labarai Peterborough.

Bristow yace yana fatan zai koyi abubuwa da dama akan imanin Musulmai, yayin da shi ma zai yi kokarin sanin inda ya sa gaba.

Haka kuma Bristow ya ce: “Zai dinga daukar kanshi a bidiyo domin bayyanawa duniya yadda yake azumi.”

“Ina fatan wannan ya zama hanyar da zai saka wasu su rungumi Ramadana kamar yadda nayi.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here