Pantami ka gayawa Buhari Arewa kwarara take da jini fah – Meenah M Sadeeq a sabon bidiyo

0
918

A yayin da hare-haren ‘yan bindiga yake cigaba da kamari a yankin Arewacin Najeriya, musamman jihohin Borno, Katsina, Zamfara, Sokoto da sauransu, mutane da yawa suna nuna takaicinsu akan irin halin ko in kula da gwamnati take nuna yayin da a kowacce rana rayuka suke salwanta.

Mutane bila adadin sun hau kafafen sadarwa sun bayyana rashin jin dadinsu akan hakan, inda suke ganin bai kamata gwamnatin tarayya ta yiwa mutanen arewa haka ba a wannan lokacin.

A nata tsokacin game da kashe-kashen, fitacciyar matar nan da tayi suna a shafin Facebook, Meenah M Sadeeq, ta aikawa da Isa Ali Pantami sako a wani sabon bidiyo mai tsawon minti uku, inda ta roke shi ya yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari bayani akan halin da yankin na Arewa ke ciki.

A cewarta akwai yiwuwar abinda ake gayawa shugaban kasar yana faruwa daban da abinda yake faruwa, ma’ana akwai yiwuwar shugaban kasar bai da masaniya akan gaskiyar abinda ke faruwa.

Meenah ta ce bai kamata duk wahalar da ‘yan arewa suka yiwa shugaba Buhari wajen jefa masa kuri’a ba ya juya musu baya a yanzu.

Meenah ta kara da cewa dalilin da ya sanya ta zabi ta bawa Pantami wannan sako, shine saboda shine yake zaune a arewa kuma yake ganin halin da arewa ke ciki, kuma ta bayar da misali da wani wa’azi da ya taba yi wanda ya dinga kuka da idonshi akan halin da arewa ke ciki, ta ce ita ma lokacin tayi wannan kuka.

Ga dai bidiyon abinda ta ce:

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here