Nicole Queen: Baturiya da tayi watsi da rayuwar gidan rawa ta rungumi Musulunci gadan-gadan

0
710

Mun kawo muku labarai kala-kala akan mutanen da suke Musulunta a fadin duniya. Amma wannan daban yake da kowanne. Wannan labarin wata Baturiya ne da tayi watsi da rayuwar gidan rawa da shaye-shaye ta kama addinin Musulunci da hannu biyu.

Tana alfahari da addinin Musulunci, tana da yara da yawa da ta basu kyakkyawar tarbiyya, ‘yar kasuwa ce, kuma ta zama daya daga cikin mata wadanda Musulmai ke koyi da su a yanzu. Ba kowa bace face Nicole Queen, ga dai takaitaccen labarinta:

Nicole Queen | Photo Source: Facebook

‘Suna na Nicole Queen, na fara girma a Louisiana, har sai dana kai kimanin shekara 8, sai muka koma wani karamin gari a yankin Kudancin Dallas Texas. Iyayena Kiristoci ne sosai, hakan ya sanya na tashi da son addinin sosai.

“Duk da dai su Kiristoci ne, amma basu da tsattsauran ra’ayi, sun yarda akwai Allah, amma kuma suna rayuwarsu yadda suke ganin yafi musu. Kakannina sunfi tsauri a addinin Kiristanci, sune suka sanya ni na tsunduma cikin addinin sosai.

“Daga baya na koma daukar hoto a birnin Dallas, kuma yawancin aikina a gidan rawa nake zuwa ina yi da daddare. Aikina shine na dauki taurari, ‘yan wasa da kuma manyan mutane idan sunje wajen casu.

‘Ba wai rayuwa ba ce da mutum zai yi alfahari da ita, domin kuwa zuwa wajen casu a koda yaushe ba abu bane mai kyau, inda komai nawa ina yin shi da daddare ne, da rana kuma sai nayi bacci. Ba rayuwa bace mai dadi kwata-kwata. Naji abubuwa da dama na damuna saboda wannan rayuwa da nake yi.

“A koda yaushe kokarin da nake na samu kwanciyar hankali, na kuma san menene yasa na zo duniyar ma baki daya, mutane da dama na ce mini rayuwata na burgesu, amma ni dai na san cewa mutanen da suke tare dani ba wai sun damu da rayuwa mai muhimmanci bane, bama su san menene ke faruwa ba game da rayuwarsu.

“A wannan lokacin da nake aiki a matsayin mai daukar hoto a cikin zuciya ta ina jin kusanci da Ubangijina a lokuta da dama. Zan iya tuna lokacin dana dinga kokarin gano ainahin abinda nake nema a rayuwa. Na san Musulmai da yawa wadanda addini bai dame su ba sosai.

‘Na fara sanin menene Musulunci daga wajen wasu daga cikin abokanai na Musulmai da basa shan giya, sannan kuma suke da rikon addini. Ina tambayarsu mai yasa bakwa zuwa wuri kaza da kaza, sai su amsa mini basa zuwa ne saboda su Musulmai ne.

‘Wata rana da daddare bayan na gama aiki, sai na hadu da mijina na yanzu Hassan, a lokacin da na kaiwa abokanai na ziyara. Shi ma yana ta fama da abinda nake ta fama dashi a zuciyata. Shi Musulmi ne, amma kuma bai damu da addinin ba. A lokacin da muka hadu mun gano cewa duka abu daya ne yake damun mu.

“Hassan ya sanar dani game da Musulunci, sannan ya bukaci na shiga makaranta domin na koyi addinin. Sai na fara ganewa Musulman da nake haduwa da su suna da jajircewa kuma sun san abinda ya kawo su duniyar ma baki daya. Sun yi daban da kowanne mutum.

“Bayan na fara koyon addinin Musulunci, sai ya shiga raina sosai. Sai na cinye dare baki daya ina kallon bidiyo a YouTube akan addinin Musulunci, musamman ma na Yusuf Estes.

“Daga baya wani abu ya fara gaya mini cewa ya kamata ki daina irin wannan rayuwar da kike matukar kina so ki san dalilin da ya kawo ki duniya. A lokacin dana fara juyawa zuwa Musulunci, naga komai yana tafiya da sauri-sauri.

“A watan Afrilun shekarar 2007, sai na yanke shawarar karbar Musulunci, sai kuwa na karbi kalmar shahada. Rayuwata ta canja tun daga wannan lokacin, Ina saka Hijabi abina, kuma ni daya ce daga cikin mambobin Musulman kasar Amurka. Musulunci da Kiristanci suna da alaka sosai, saboda haka shigowata Musulunci naji kamar na bar gida ne na shiga wani gida.

“Tun daga nan ni da mijina Hassan muka fara aiki tukuru a cikin birnin Dallas.

Nicole Queen ta zama mai watsa shiri da ita da Monica Traverzo a ‘Salam Girl”. Shiri ne akan mata Musulmai.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here