Naziru Sarkin Waka ya mayarwa da El-Rufai martani kan batun cire mazakutar masu fyade

0
581

A makon da ya gabata ne dai BBC Hausa ta ruwaito cewa gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya bukaci da a dinga yiwa masu fyade dandaka.

Gwamnan ya ce hanya daya da za a iya magance wannan matsala ita yi wa masu aikta wannan laifi dandaka.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wajen wani taro da aka gabatar na yanar gizo ta hanyar amfani da manhajar Zoom a ranar Asabar din da ta gabata.

Taron dai an gabatar da shine domin neman hanyar da za a kawo karshen matsalar fyaden da taki ci taki cinyewa a fadin Najeriya.

A cikin harshen turanci gwamnan ya ce “Remove the tools”, ma’ana a cire kayan aikin.

Haka kuma gwamnan ya kara da cewa a jihar Kaduna an samu karuwar fyade, inda ya bayyana cewa a cikin ‘yan kwanakin nan an yiwa mutane 485, kamar dai yadda alkaluma suka nuna.

Sai dai Naziru Sarkin Waka ya soki wannan ra’ayi na gwamnan jihar, inda ya nuna cewa sam hakan bai kamata ba ace irin wannan maganar ta fito daga bakin mutum kamar sa ba, inda ya wallafa cewa:

Naziru dai ya jima yana yin wannan ikirari na cewa a koma ga Allah a daina fidda tsiraici, inda ya ce hakan shine hanyar da za a magance matsalar fyade.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here