Nazir Sarkin waka ya nemi afuwa kan kuskuren da ya tafka wajen yiwa Ali Nuhu ta’aziyya

0
1038

A shekaran jiya Allah ya yiwa Nuhu Paloma mahaifi ga shahararren jarumi a masana’antar Kannywood da Nollywood rasuwa wato Ali Nuhu, inda masana’antar ta cika da alhinin wannan babban rashi da aka yi mata.

Sai dai wani abun da yasa mutane a duhu shine yadda ake yiwa Ali Nuhu gaisuwa da wani salo da ba’a saba gani ba, ma’ana ba a yiwa mahaifin na Ali Nuhu addu’ar neman tsira sai dai shi Ali Nuhun da ake yiwa jaje da addu’ar Allah ya bashi hakurin juriyar rashin da yayi, wanda wasu suka danganta hakan da cewa mahaifin Ali Nuhun ya kasance mabiyin addinin kiristanci ne ba Musulmi ba kuma haramun ne rokawa wanda ba Musulmi ba rahama.

A irin haka ne Hafsa Idris Barauniya ta wallafa a shafinta ita ma irin wannan addu’a da jaje ga Ali Nuhu, inda aka dinga yi mata tsokaci a kasa inda ciki har da Nazir Sarkin Waka a cikin masu tsokacin sai dai nasa tsokacin ya zunguro sama da kara.

Nazir Sarkin Waka yayi tsokaci da ‘Oh Good Allah ya bashi hakurin rashi’, jim kadan da yin wannan rubutu nasa kuwa aka yi masa caa akan me zai sa ya nuna jin dadin sa bayan rashin aka ce an yiwa Ali Nuhu, wasu kuma na goyon bayan sa da cewa ai ba Musulmi bane dan bai ce Allah ya jikan shi ba ba laifi bane.

Sai dai ganin cewa karamar magana ta zama babba yasa Nazir Sarkin Waka ya kwafo rubutun ya wallafa a shafinsa gami da zagaye iya inda yayi kuskuren gami da wayarwa da mutane kai kan cewa shi fa ga ma’anarsa kenan ba tuntuben alkalami aka samu ya so ya rubuta ‘Ow God’ ma’ana ‘Wayyo Allah’ shine ya kuskure ya rubuta ‘Oh good’ ya kuma nemi ayi masa afuwa.

Sai dai har ya zuwa yanzu Ali Nuhu bai wallafa labarin rasuwar mahaifin nasa a shafinsa ba, wala’Allah don gudun irin wadannan kananan maganganu yasa bai ce komai akan rasuwar ba ko kuma wani dalili daban.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here