Najeriya ta zama kasa ta 5 a duniya da al’ummarta suka fi kashe kansu

0
330

Rahotanni sun nuna Najeriya ce kasa ta biyar a duniya da mutane suka fi kashe kansu, inda a kowanne wata ake samun mutum shida a kalla da suke kashe kansu. Guba ita ce yawancin abinda mutane ke amfani da ita wajen kashe kansu a Najeriya.

Bayan haka kuma, an ruwaito cewa yawancin kisan kan da ake samu a Najeriya a tsakanin matasa na da nasaba da shan miyagun kwayoyi, wanda ya zama tamkar ruwan dare a tsakanin matasan Najeriya.

A yanayin yadda abubuwa suke tafiya yanzu a Najeriya, idan har ba a dauki mataki ba, akwai yiwuwar Najeriya za ta dinga rasa sama da mutane 100 a kowacce rana sanadiyyar shan miyagun kwayoyi. Hakan ya biyo bayan yawan ‘yan Najeriya ya kai kimanin kashi 3 cikin 100 na al’ummar duniya, sannan kuma Najeriya ita ce take da kashi 6 cikin 100 na masu shan tabar wiwi a duniya.

Haka kuma wani rahoton ya bayyana cewa kashi 14 na mutanen duniya da suke amfani da kwayoyin Tramadol da Codeine duka ‘yan Najeriya ne.

Haka kuma babban abin damuwa a Najeriya din shine wani shafin yanar gizo da ake amfani da shi mai suna ‘Dark Net’ da ake saye da sayarwar miyagun kwayoyi kuma har yanzu aka kasa gano masu amfani da wannan shafi.

Sai kuma sarrafa kwayoyin da ake yi a kasar, a kwanakin baya hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta gano wasu wurare da ake sarrafa kwayoyin a jihohin Plateau, da Legas, inda aka gano cewa mallakin wasu mutanen kasar Sin ne da Jamus.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here