Naira 6,000 ‘yan bindiga suke biyan mu suyi zina da mu – Binta da Bilki yaya da kanwa da jami’an tsaro suka kama

0
222

Jami’an hukumar Civil Defence sun kama wasu ‘yan mata yaya da kanwa, Binta Hussaini da Balki Hussaini, ‘yan garin Konni dake Jamhuriyyar Nijar.

An kama ‘yammatan ne sanadiyyar dangantakar dake tsakaninsu da shugaban ‘yan bindiga dake dajin Bagega na karamar hukumar Anka dake jihar Zamfara, wanda aka fi sani da Shaho, da kuma abokinshi Jijji. Binta wacce tayi magana da manema labarai ta bayyana dangantakar dake tsakaninsu da ‘yan bindigar.

Ga dai yadda ta kasance tsakaninsu:

A ina kuke da zama?

“Muna zaune a unguwar Sabon Gari dake karamar hukumar Kaura-Namoda, cikin jihar Zamfara. Mu ‘yan asalin garin Konni ne dake Jamhuriyar Nijar.

Mai kuke yi a Najeriya?

“Muna zaune da iyayenmu ne da suke sakar tabarma suna sayarwa.

An kama ku a kauyen Bagega tare da dan acaba, shin mai kuke yi a Bagega?

“Yan bindiga ne suka gayyace mu muje suyi zina da mu. Sun bukaci dan acabar ya kai mu wurin da suke.

Nawa suke biyan ku idan suka yi zina da ku?

“A lokuta da dama suna biyan mu naira dubu shida (N6,000), wani lokacin kuma su bamu naira dubu bakwai (N7,000).

Sau nawa kuka yi lalata da su?

“Sau hudu kawai, bamu taba ganin iyalansu ba.

Suna baku abinci idan kuka shiga dajin kuna tare da su?

“Eh, suna bamu abinci.

Daga yaya kuka san ‘yan bindigar?

“Suna zuwa gidanmu a Kaura-Namoda su kwanta da mu. Amma lokacin da suka bukaci muje wajensu sun ce a kai mu garin Anka ne mu jira dan acaba wanda zai kai mu inda suke a cikin daji. Sai kuma gashi an kama mu a lokacin da muke kan hanyar zuwa.

Shin iyayenku sun san abinda ke tsakaninku da ‘yan bindigar?

“A’a, basu san muna zuwa muyi lalata da ‘yan bindigar ba.

Me kuke yi da kudin da ‘yan bindigar suke baku?

“Muna amfani da kudin mu sayi kayan abinci mu bawa iyayenmu, saboda talakawa ne.

Yaushe ne kuka zo Najeriya?

“Farkon shekarar da ta gabata muka zo Najeriya.

Karshen hirar ta su kenan, Allah ubangiji ya kare mu ya kuma cigaba da tona musu asiri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here