Naira 500 ake bani duk lokacin dana kashe mutum – Matashi

1
3571

Rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ta kama wani matashin saurayi dan shekara 19 mai suna Sunday Sodipe, da hannu a kisan wasu mutane 6 a karamar hukumar Akinyele dake jihar a cikin watan Yuni, 2020.

A ranar Juma’ar da ta gabata, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Nwachukwu Enwonwu, ya gabatar da Sodipe a helkwatar hukumar dake Eleyele, Ibadan.

Sodipe ya bayyana cewa yana yiwa wani mai maganin gargajiya aiki ne mai suna Adedokun Yinusa Ajani, wanda ke da shekaru 50, wanda shine yake sa shi yana yin wannan aika-aika.

Da yake amsa tambaya daga wajen manema labarai, matashin ya ce shi ya kashe Barakat Bello, mai shekaru 18 a ranar 1 ga watan Yuni, 2020, sannan kuma shi ya bugawa Mrs Azeezat Somuyiwa dutse a kai ya kasheta a ranar 5 ga watan Yuni, 2020, ya dauke wayarta ya siyarwa da wani mai suna Shehu Usman.

Sodipe ya kara da bayyana cewa shi ya kashe Grace Oshiagwu mai shekaru 21 a ranar Asabar 13 ga watan Yuni, 2020, haka kuma yana da hannu a kisan wani yaro dan shekara biyar mai suna Mujib Tirimisiyu a ranar 22 ga watan Yuni, 2020.

Matashin ya ce kisan da yayi na karshe shine a ranar 29 ga watan Yuni, inda ya kashe wata mata mai suna Adeola Azeezat, mai shekaru 45 da yarta Dolapo mai shekaru 23.

Matashin saurayin ya ce a duk lokacin da zai fita wannan aiki na shi, uban gidan nashi yana sanya shi ya durkusa a gaban shi yayi wasu maganganunshi na siddabaru, sannan ya sanya wani abu a bakinshi sau uku.

Sodipe ya ce a duk lokacin da ya samu wanda zai kashe yana amfani da shebir ne ya buge, idan suka fadi cikin jini sai ya karanta wani siddabaru ya zagaye gawarsu sau uku yayin da idon shi yake rufe kafin ya bar wajen.

Ya ce bayan ya gama aikinshi yana komawa wajen bokan ne, sai ya sake karanta wasu siddabaru, sai ya siya masa abinci ya bashi naira dari biyar (N500).

Da aka tambayeshi dalilin da ya sanya yake kashe mutane, saurayin yace shi ma bai sani ba, shi dai kawai yana bin umarnin bokan ne.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here