Nafi jin farin ciki da nutsuwa bayan shigowa ta Musulunci – Jaruma Adunni Ade

0
212

Kwanan nan ne fitacciyar jarumar fina-finan Kudancin Najeriya, Adunni Ade, ta bayyana cewa ta fita daga addinin Kiristanci ta koma addinin Musulunci.

A cewar ta, ta fi jinta cikakkiya kuma cikin farin ciki a yanzu fiye da yadda take a baya.

Bayan wallafa wani dogon rubutu a shafin Instagram, ta ce: “Kun san mai yasa bana yawan yin magana akan addini? Saboda ina cikin damuwa sosai, sanadiyyar son zuciya da ya addabe ni. Sai kana da kusanci dani sosai zaka gane abinda nake yi.

“Gare ku wadanda suka damu su suke kuma faman tambaya, Kwarai ni Musulma ce. Iyayena Musulmai ne kuma an dora ni akan hanyar Musulunci.

“Mahaifina Musulmi ne, wanda ya bawa ‘ya’yanshi damar zabar duk addinin da suke so tsakanin Musulunci da Kiristanci. Mahaifiyata Kirista ce, duk da dai bata bin addinin Kiristancin. Kishiyar mahaifiyata ita ma Kiristace, ‘yan uwana mata duka Kiristoci ne, dan uwana namiji Musulmi ne.

“Shin na taba zuwa coci? Naje coci masu yawa. Akwai lokacin dana taba komawa addinin Kiristanci, amma wani abu dana sani shine tun lokacin Musulunci bai bar jikina ba. Duk wasu abubuwa da nake yi na Musulmai nake yi.

“Ina cikin fargaba akan yadda mutane zasu dauke ni idan na koma Musulunci a wancan lokacin. Shekara hudu da suka wuce na yanke shawarar yin rayuwar dana ga ta dace dani. Ni daya na dawo addinin Musulunci. Na jini cikakkiya, cikin farin ciki. Na samu albarkar rayuwa. Babban dana Musulmi ne, yana sallah da azumi.

“Ina saka duk kayan dana ga dama. Babu wanda ya isa ya gaya min abinda zan yi. Ba komai bane dan kun yi ta maganganu a kaina, amma wadanda suka sanni sun san yadda nake.

“A yadda na koya a Musulunci, Allah zai yi mana hukunci akan abinda muke yi, ba abinda mutane suka ga muna yi a fili ba.

“Ba wai ina neman suna a wajen mutane bane. Ina so kowa yayi rayuwarshi yadda ta dace. Ka fita harkar duk wanda suke magana a kanka.

“Kamar yadda Musulmai suka sani, a watan Ramadana, Allah yana bude kofofin rahama, saboda haka duk addu’ar da muka yi karbabbiya ce.

“Muyi amfani da wannan damar a wannan shekarar. Ina rokon Allah ya sanya albarka a rayuwata wannan shekarar dama shekaru masu zuwa. Ina fatan na fadi duk abubuwan da ya kamata ku sani.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here