Na tabbata ba Buhari ne ke rike da ragamar mulkin Najeriya ba – Wole Soyinka

0
2663

Fitaccen marubucin Najeriya, Farfesa Wole Soyinka, ya ce har yanzu bai yadda cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne yake rike da ragamar mulkin Najeriya ba.

Soyinka ya bayyana haka ne a ranar Alhamis 4 ga watan Yuni a lokacin da yake hira da gidan talabijin na Plus TV Africa.

Wannan sharhi na sa ya biyo bayan budaddiyar wasikar da Kanal Umar Dangiwa (Rtd), ya rubutawa shugaban kasar a makon da ya gabata.

Dangiwa dai ya zargi shugaban kasar da nuna bambanci, musamman wajen bayar da mukaman gwamnati.

Da aka tambayeshi mai zai ce dangane da wannan wasika, Soyinka ya ce: “Abinda zan fara cewa shine godiya ga mutanen kirki irinsu Umar, wanda suke da fitowa kiri-kiri su fadi gaskiya ba tare da nuna son kai ba.

“Nayi mamaki matuka lokacin dana ga wannan. Amma na cewa kai na mai yasa zanyi mamaki bayan na jima da sanin cewa wannan abu na faruwa a kasar nan.

“Ina ganin ya kamata a hukunta wadanda ke da alhakin wannan aika-aikar. Bai kamata kawai ayi magana akan lamarin kuma ayi shiru ba.

“Na sha fadar wannan, ban tunanin akwai wanda yake rike da ragamar mulki a fadar shugaban kasa. Kuyi hakuri amma dole zan bayyana wannan, sama da shekara daya ina nazari akan wannan, kuma na tabbata shugaba Buhari ba shine yake da rike da ragamar mulkin Najeriya ba, na yarda da hakan ta fannoni da dama.

“Ba wai fadar gaskiyar ba ce kawai, mun riga mun san tarihi irin wannan. Mun san irin abinda hakan ya jawowa kasar mu, kuma mun san cewa lamarin ba wai ya zo karshe ba kenan. Kun ce kuna gabatar da bincike. Na tabbata mutumin nan ba shine yake rike da Najeriya ba.”

Soyinka ya kuma koka akan shirun da fadar shugaban kasa tayi game da maganar da Dangiwa yayi, inda ya ce hakan na neman tabbatar da maganarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here