Na sayar da kwamfuta ta na kai budurwata wajen cin abinci, bayan ta ci ta koshi tace wallahi ba ta sona – Saurayi ya koka

0
215

Wani saurayi mai amfani da shafin Twitter, ya bayyana yadda ya sanar da kwamfutar shi domin ya kai budurwarshi wajen cin abinci mai tsada.

Sai dai lamarin na su bai kare da kyau ba, domin kuwa budurwar ta ce bata son shi bayan ta ci abincin ta koshi.

Saurayin mai suna @Mrfab_ ya bayyana cewa lamarin ya faru a ranar masoya ta duniya wato Valentine’s Day a turance.

A cewar Mr Fab, yana matukar son budurwar, sai ya yanke shawarar bayyana mata soyayyarshi a ranar masoya ta dunuya, inda ya dauke zuwa wajen cin abinci mai tsadar gaske.

Saurayin yayi wannan bayani ne a wani sharhi da yayi kan rubutun da mawaki Erigga yayi, inda ya tambayi masoyansa da su bayyana abu marar dadi da suka taba fuskanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here