Na kwanta da samari sama da 62, amma duk cikinsu babu wanda ya nuna zai aure ni – Kyakkyawar Budurwa ta koka

0
1041

Budurwa da ta kwanta da maza sama da 62 ta bayyana cewa duk cikinsu babu wanda ya nuna zai aureta.

Budurwar mai suna Miss Angela mai shekaru 26, ta ce rayuwar da tayi a baya na damunta sosai.

Budurwar ta bayyana cewa abinda yafi damunta shine ganin yadda take da kyau son kowa kin wanda ya rasa, amma ba ta san mai yasa kowa yake juya mata baya ba.

Budurwar ta ce a lokacin da take Jami’a ta kwanta da malamai sama da 12, kuma rayuwar da tayi a jami’a babu dadin ji ko kadan.

“Na kwanta da malaman jami’a sama da 12, sannan na kwanta da samari sama da guda 50,” cewar budurwar.

Budurwar ta bayyana yadda tayi amfani da jikinta ta dinga rabawa malamai har ta samu ta kammala jami’a da sakamako mai kyau.

Sai dai ta bayyana cewa hankalinta ya tashi ne a lokacin da aka sanar da ita a asibiti cewa mahaifarta ta lalace saboda zubar da ciki da ta dinga yi.

Angela ta bayyana yadda tayi aure daga baya amma mijinta ya koreta bayan ya gano cewar mahaifarta ta lalace.

A karshe Angela ta bayyana cewa a yanzu haka rayuwa tayi mata wuya kuma ta riga ta sanya a ranta baza ta kara yin aure ba har abada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here