Mutumin da yake da ciwon hauka ne kawai zai iya mulkar Najeriya ta tafi yadda ya kamata – Tsohon gwamnan Oyo Alao Akala

0
1373

Tsohon gwamnan Oyo, Cif Adebayo Alao-Akala, ya ce duk wanda zai mulki Najeriya ta tafi yadda ya kamata dole sai yana da ciwon hauka ko yaya yake.

A cewar shi, Najeriya tana bukatar irin wannan mutumin wanda zai yi abu koda hakan zai jefa mutanen dake kusa dashi cikin wani hali.

Ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da jaridar Punch a ranar Asabar, a lokacin da yake bayyana kyawawan halayen da ya kamata ace shugaba yana da su.

Alao-Akala, wanda ya cika shekaru 70 a ‘yan kwanakin nan, ya kara da cewa dole sai kuma wannan shugaba ya kasance bashi da nuna bangaranci.

Ya bayyana tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a matsayin irin wannan shugaba da ya kamata Najeriya ta samu a wannan lokacin.

“Muna da shugabanni na gari, amma shugabannin mu ba a barinsu suyi abinda ya kamata suyi. Muna bukatar shugaba da yake da dan tabin hankali da zai iya jagorantar mu.

“Muna bukatar shugaban da zai yi abu ba tare da tunanin abinda zai faru dana kusa dashi ba.

“Muna bukatar shugaban da zai yi abinda ya kamata. Kayi abinda ya kamata ba abinda kowa yake so ba. Zai iya zama mutane na so amma kuma ba shine daidai ba. Amma idan kuma ba abinda mutane ke so bane kuma shine daidai watarana mutane za su ji dadi sosai.

“Har yanzu bamu samu mutanen da suka san ainahin abinda yake faruwa a Najeriya tun bayan mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

“Shekaru na 70 yanzu na ga duk abinda ke faruwa. Obasanjo yayi iya yinsa; amma mutum tara yake bai cika goma ba. Obasanjo Bayerabe ne, amma kunga wani Bayerabe da ya karu da shi a gwamnatinsa? Shi kawai yana daukar kanshi a matsayin dan Najeriya ne ba ruwanshi da bangaranci,” cewar Alao-Akala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here