Mutum 6 sun nutse a kogi a yayin da suke kokarin tsira da ransu daga hannun ‘yan bindiga a Katsina

0
886
​What To Do When Someone Is Drowning​

A wani rahoto da Sahara Reporters ta fitar ya nuna cewa akalla mutane bakwai ne suka rasa rayukansu a wani sabon hari da aka kai kauyukan Kasai da Nahuta dake karamar hukumar Batsari cikin jihar Katsina a ranar Juma’a da daddare.

Wata majiya daga Batsari, da tayi magana da Sahara Reporters, ta bayyana cewa mutane shida daga cikinsu sun nutse a cikin kogi ne ciki hadda wata mata mai ciki a lokacin da suke gudun tsira da rayukansu.

Ya ce ‘yan bindigar kuma sun kashe wani mutum guda daya a yayin harin, inda kuma aka nemi mutane biyu aka rasa.

An ruwaito cewa mutanen kauyen sun gudu cikin daji ne don gujewa harin ‘yan bindigar.

Majiyar ta ce ‘yan bindigar sun kai hari kauyukan akan babura ne dauke da manyan makamai.

Sahara Reporters ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun shafe awanni da yawa a cikin kauyukan suna cin karensu babu babbaka ba tare da jami’an tsaro sun kai dauki ba.

Majiyar ta ce: “An samu gawarwakin mutane shida a cikin kogi ranar Asabar da safe, anyi ruwan sama mai karfi a wannan ranar, kuma daya daga cikinsu mace ce mai ciki. Mahaifina shine ya sanar da Sarkin Ruwa, wanda ya cewa mutane su duba cikin kogin kafin nan aka samo gawarwakinsu.

Kauyen dai yana da nisan kilomita shida daga garin Batsari.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here