Mutum 3,000 za su dinga mutuwa kullum a kasar Amurka a wannan watan – Gwamnatin kasar Amurka

0
161
President Donald Trump listens as Louisiana Republican gubernatorial candidate Eddie Rispone speaks during a campaign rally at the CenturyLink Center, Thursday, Nov. 14, 2019, in Bossier City, La. (AP Photo/ Evan Vucci)

Wani hasashe da gwamnatin kasar Amurka tayi ya bayyana cewa akalla mutane dubu uku ne za su dinga mutuwa a kowacce rana a wannan wata na Mayu da muke ciki, inda kuma mutum dubu dari biyu zasu kamu da cutar Coronavirus a kowacce rana.

Rahoton na sirri na gwamnatin kasar wanda jaridun New York Times da Washington Post suka wallafa, ya kwatanta wannan rahoto da abinda ke faruwa a yanzu da ake samun mutum 25,000 zuwa 30,000 da suka kamu da cutar, inda kuma ake samun mutum 1,500 zuwa 2,000 da suke mutuwa a kullum.

Har ya zuwa yanzu dai fadar shugaban kasar ta Amurka ba ta yi magana ba akan lamarin, wanda yaci karo da hasashen Donald Trump a baya da yace baya tunanin mutanen da za su mutu sanadiyyar cutar a kasar Amurka za su wuce 100,000.

Duka wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar ta Amurka, Donald Trump yake zargin kasar China da kirkirar cutar ta coronavirus wacce tabi ta addabi duniya a wannan lokacin.

Trumo dai ya kafe akan maganar shi ta cewa kirkirar cutar aka yi duk kuwa da cewa kwararru a fannin lafiya sun bayyana cewa wannan cuta daga Allah take, ba wani ne ya kirkiro ta ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here