Mutane sun cika da mamaki bayan saurayi ya bayyana yadda ya fara sana’ar kiwon kaji da naira 11,000 kacal

0
961

Wani rubutu da aka wallafa a shafukan sadarwa ya burge mutane da yawan gaske, inda wani saurayi wanda aka bayyana sunanshi na Twitter da @ydb_ZN, ya nuna yadda ya fara kasuwancinsa, inda mutane da yawa suka yi ta magana a kai.

A ranar Asabar ne @ydb_ZN, wanda ya mallaki gonar kaji ta Khondlo Poultry Farm, ya wallafa hotunan gonar tashi, inda kuma ya bawa sauran masu amfani da kafar sadarwa shawara.

“Shawara ta ga wanda yake so ya fara kiwon kaji, daga samar da kwai, da kuma kaji. Ana iya daukar kwanaki 35 kafin kaji su rika su isa kai wa kasuwa, inda kuma kanana suke daukar mako 18 zuwa 20.

Post source: @ydb_ZN Twitter Page

Jim kadan bayan wallafa wannan rubutu na shi mutane suka yi caa akan shi da tambayoyi.

Inda a cikin amsa guda daya ya bayyana musu cewa ya fara wannan kasuwanci na shi da naira dubu sha daya da dari hudu kacal (N11,400).

Ya ce: “Ba sai ka tara da yawa ba, zaka iya farawa da dan abinda ke hannunka…Ranar dana fara ina da R500 ne kawai, na kashe kimanin R2000 kimanin N45,000 har suka girma.

Post source: @ydb_ZN Twitter Page

A wani rubutu da ya sake wallafawa @ydb_ZN, ya nuna cewa saboda yadda ya samu sa’a a wannan kasuwancin nashi, an nemi ayi hadin guiwa dashi da kudi kimanin naira 230,000 yaki amincewa, inda ya ce cikin sauki zai samu wannan kudi da wannan kasuwanci.

Post source: @ydb_ZN Twitter Page

Wannan kasuwanci na @ydb_ZN ya burge su matuka, inda suka dinga yaba masa.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka:

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here