Musulunci ne abinda ya ragewa duniya a wannan lokaci na duhun kai – Cewar shugaban babbar jam’iyyar kasar Hungary

0
578

Shugaban wata babbar jam’iyyar siyasa a kasar Turkey, ya bayyana cewa Musulunci shine abinda ya rage a duniyar nan a wannan lokaci da kowa ya shiga duhun kai.

Shugaban jam’iyyar ya kai ziyara kasar Turkey, inda ya ziyarci jami’o’i da yawa a kasar.

“Ba mu zo kasar Turkey domin mu kara kulla alaka ta dimokuradiyya ko tattalin arziki ba, mun zo ne domin mu hadu da ‘yan uwanmu maza da mata,” cewar Gabor Vona, shugaban jam’iyyar, kamar yadda islametinfo.fr ta ruwaito.

Kamar yadda majiyar ta ruwaito, shugaban jam’iyyar ya bayyana cewa kasashen yamma basa son yadda yake goyon bayan kasar Turkey, Azerbaijan da sauransu.

Haka kuma Gabor Vona ya tabbatar da cewa jam’iyarshi bata goyon bayan kungiyoyi da suke nuna kyamar Musulunci a kasashen Turai.

Shugaban jam’iyyar ya kuma bayyana cewa, mutanen kasar Turkey da suka ginu akan kaunar juna, girmama al’ada da kuma nuna kishin kasa, babban abin misali ne ga kasar Hungary.

A cewar Gabor Vona, alakar dake tsakanin Hungary da Turkiyya ta samo asali ne daga amintaka ba wai kawai abokantaka bane.

Kamar yadda islametinfo.com ta ruwaito, shugaban jam’iyyar ya jaddada a lokuta da dama cewa “Musulunci shine abinda ya rage ga al’ummar duniya a wannan lokaci da mutane ke cikin duhu.

Haka kuma akan muhimmancin addinin Musulunci, Gabor Vona ya bayar da tabbaci a shafin yanar gizo na jam’iyyarsu.

“Afirka ba ta da wani tasiri a duniya; Australia da kudancin Amurka suna fama da rikice-rikice saboda yawan al’ummarsu. Idan aka yi la’akari da wannan, abu daya ne ya ragewa duniya, shine Musulunci.”

Bugu da kari, Vona ya kara da cewa ya tsunduma cikin kaunar Musulunci da Musulmai sanadiyyar abokai da abokanan aiki da ya hadu dasu a rayuwarsa. Babban abin mamaki shine, daya daga cikin manyan shaidu a wajen bikinsa dan kasar Palastine ne, wannan abu da yayi ya fusata abokanan hamayyarsa.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here