Musulmi a kasar Bosnia sun yi taron tunawa da kisan karen dangin da aka yiwa al’ummar Musulmi a kasar shekaru 25 da suka wuce, wanda aka sanyawa suna ‘Kisan Srebrenica’, kisan da aka bayyana cewa shine mafi muni da aka taba yi a yankin nahiyar Turai tun bayan yakinduniya na biyu.

Mutanen da suka gabatar da wannan taro na kisan, sun bijirewa dokar da gwamnatin kasar ta sanya domin dakil yaduwar cutar coronavirus.

A ranar 11 ga watan Yulin shekarar 1995 ne sojojin Sabiya suka kashe Musulmi maza manya da kanana sama da mutum dubu takawas (8,000) a cikin ‘yan kwanaki kalilan, wannan kisa dai ya girgiza duniya baki daya.

Sehad Hasanovic matashi mai shekaru 27 yana daga cikin al’ummar Musulmi 3,000 da suka samu damar halartar wannan taro a jiya 11 ga watan Yuli, Sehad ya ce akwai takaici sosai kaga wasu suna kiran iyayensu kai kuma baka da wanda zaka kira.

Manyan kotunan Majalisar Dinkin Duniya guda biyu sun bayyana wannan kisa na Srebrenica a matsayin kisan kare dangi, bayan yakin da aka gabatar tsakanin Kroshawa da Sabiyawa Musulmi, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 100,000.

A halin yanzu dai an binciko gawar mutane 6,900 da aka kashe daga cikin manyan kaburbura guda 80 da aka sanya su a ciki.

Sakamakon wannan kisa dai an yankewa janar Ratko Mladic da Radovan Karadzic hukuncin daurin rai da rai a kotun duniya, sanadiyyar gudummawar da suka bayar a lokacin.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here