Mun rufe Masallatai a Bauchi, amma har yanzu mutane na sha’awar zuwa sallar Juma’a saboda basu yadda da Corona ba – Bala Muhammad

0
146

Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed, ya bayyana cewa har yanzu mutanen jihar Bauchi basu yadda da cewa cutar Coronavirus gaskiya bace duk kuwa da cewa shi ma dakyar ya sha.

Da yake magana a gidan talabijin na NTA a jiya Litinin 11 ga watan Mayu, gwamnan ya ce tantama da karyata wanzuwar cutar ita ce take kara sanya mutane cikin hadari a jihar.

Ya ce: “Daya daga cikin matsalar da muke fama da ita a jihar Bauchi ita ce, tantama da karyata cutar, saboda har yanzu mutane basu ma yadda da cewa cutar gaskiya bace.

“Ni kuma na gaya musu, ina ganin saboda Allah ya bayar da misali a jihar shine yasa cutar ta fara ta kaina. Cutar ba ruwanta da mukami ko kudi, dakyar na samu na sha data kamani nima.

“Saboda haka ya kamata mutane su dauki wannan cuta da gaske. Mun kulle Masallatai da coci amma mutane suna so suje sallar Juma’a, suna zuwa kasuwanni ba tare da kare kansu ba.

A daya bangaren kuma gwamnan yayi magana akan maganin zazzabin cizon sauro na Chloroquine, inda ya ce:

“Ba zan ce kowa yayi amfani da Chloroquine ba, ni ba likita bane, kuma ba mahaukaci bane da zance mutane suyi amfani da magani, bani da wannan ikon.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here