Mun raba zunzurutun kudi Naira biliyan 43.4 ga jihohi 24 na Najeriya – Gwamnatin tarayya

0
527

Gwamnatin tarayya ta raba zunzurutun kudade da yawansu ya kai naira biliyan 43.416 a matsayin tallafin aiwatar da ayyuka ga jihohi 24 da suka cancanci haka a sakamakon da aka samu a shekarar 2018 karkashin tsarin bayar da tallafi da Bankin Duniya yake yi ga kasashen duniya.

Ministar kudi ta Najeriya, Mrs. Zainab Ahmed, ita ce ta bayyana haka a wata sanarwa da daraktan ma’aikatar labarai da hulda jama’a, Mr. Hassan Dodo, ya sanya hannu a ranar Laraba.

A cewar ministar, jihohin guda 24 da suka aka baiwa wannan tallafi sun hada da jihar Abia, Adamawa, Bauchi, Benue, Delta, Edo, Ekiti, Enugu, Gombe, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Niger, Ondo, Ogun, Oyo, Sokoto, Taraba da jihar Yobe.

Ta yi bayanin cewa bayar da kudin ga jihohin 24 ya biyo bayan cancantar da suka yi a tsarin da aka gabatar na shekara, wanda ofishin audita janar na gwamnatin tarayya ya gabatar a matsayin hanyar tabbatar da cancantarsu.

Ministar ta bayyana hanyoyin da jihohi za su bi domin samun damar cancanta wajen samun tallafi, inda ya hada da wallafa kasafin kudin shekara a yanar gizo, da kuma wallafa yadda aka kashe kudin shekarar da ta gabata.

Sauran sun hada da inganta hanyar kashe kudade da kuma rage asarar kudaden shiga da kuma bude asusun bai daya, wato Single Treasury Account, karfafa hanyoyin karbar kudaden shiga da dai sauransu.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here