Mun dauka Musulmi ne kai, saboda mun ganka da gemu – Cewar ‘yan sandan Indiya da suka yiwa lauya dukan tsiya a tunaninsu Musulmi ne

0
335

Bayan ‘yan sanda sun yiwa lauya Deepak Bundele dukan tsiya a ranar 23 ga watan Maris a lokacin da yake kan hanyar zuwa asibiti a garin Betul dake Madhya Pradesh, ya cigaba da daukaka kara akan abinda ‘yan sandan suka yi masa.

A lokacin da suke kokarin kare kansu, ‘yan sandan sun bayyana cewa kuskure aka samu, sun dake shi ne a tunanin da suke yi na cewa shi Musulmi ne.

A hirar da aka dauka ta Bundele wacce aka wallafa a shafukan sadarwa, an jiyo muryar jami’an ‘yan sandan suna cewa sun kai masa hari ne bisa kuskure, saboda wasu daga cikinsu sunyi tunanin shi Musulmi ne saboda sun ganshi da gemu.

“Dukan mu munji kunya saboda mun yiwa dan uwanmu mai bin addinin Hindu irin wannan abu ba tare da sanin ko shi waye ba.

“Bamu da wata matsala tsakaninmu da kai. Duk lokacin da aka samu rikici tsakanin Musulmai da Hindu, koda yaushe ‘yan sanda suna tare da masu bin addinin Hindu; hatta su kansu Musulman sun san da haka. Amma duk abinda ya faru da kai ya faru ne a bisa rashin sani. Saboda haka bamu san mai zamu ce maka ba,” ya ce.

Dan sandan ya cigaba da cewa, “mutumin da ya dake ka Kattar ne, shine yake azabtar da Musulmai a duk lokacin da aka kama su.”

Bundele ya ce har yanzu ba a yiwa wannan korafi da ya shigar rijista ba. “Na kasa yin komai bayan ‘yan sandan sun bani hakuri. Shin ko ni Musulmi ne wace doka ce ta bawa ‘yan sandan damar cin zarafin Musulmai ba tare da wani laifi ba,” ya ce.

Bundele ya ce yana kan hanyarsa ta zuwa asibiti ne a ranar 23 ga watan Maris don duba lafiyarshi, inda aka bayyana dokar hana zirga-zirga. Yana cikin tafiya kawai sai ‘yan sanda suka tsare shi a tsakiyar hanya.

Da ya bukaci ‘yan sandan su gabatar da aikinsu akan dokar kasa, sai suka zage shi suka kuma zagi dokar kasar baki daya suka fara dukan shi da kulki, ya sanar da The Wire.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here