Muhammed Goni: Gwamnan farar hula na farko a jihar Borno ya koma ga Allah

0
319

Wani rahoto da muka samu ya nuna cewa Muhammad Goni, wanda yake shine gwamnan farar hula na farko a jihar Borno ya koma ga Allah.

Marigayin dan siyasar na da shekaru 80 a lokacin da ya koma ga Allah, inda ya mutu a Asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri da misalin karfe 8 na daren jiya Laraba.

Dan uwan tsohon gwamnan, Lawan Kareto, wanda yake yanzu dan majalisar jiha ne a jihar ta Borno, shine ya bayyanawa Premium Times rasuwar ta shi.

“Mun rasa masoyi kuma dattijon kirki a cikin wannan daren.

“Mun gode Allah da irin rayuwar da yayi. Kayi rayuwar da zaka haura shekaru 80 a duniya ba karamin dama ce Allah ya baka ba. Allah ya jikanshi da rahama.”

An zabi Muhammed Goni, gwamnan jihar Borno a shekarar 1979, amma ya fadi takara a lokacin da ya fito a karo na biyu a shekarar 1983.

Haka kuma ya sake fitowa takarar gwamnan jihar ta Borno a karkashin jam’iyyar PDP a shekarar 2011, amma a lokacin tsohon gwamnan jihar Kashim Shettima, ya lashe zabe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here