Mu Katsina ba Coronavirus ce damuwar mu ba, ‘yan bindiga ne suka addabe mu – Gwamna Masari

0
235

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya roki jami’an tsaron Najeriya da su taimaka su ceto rayukan al’ummar jihar daga hannun ‘yan bindiga da suka addabe su.

Gwamnan ya koka akan wannan hare-hare da ‘yan bindigar suke kai musu, bayan ziyarar da shugaban tsaro na Najeriya, Leo Irabor, da sauran manyan jami’an tsaron Najeriya daga helkwatarsu ta Abuja.

Gwamna Masari wanda ya bayyana cewa hare-haren da ‘yan bindigar suke kaiwa jihar yana nema yayi yawa, yace mutanen jihar suna zaune cikin dar-dar, bayan ‘yan bindigar sun kashe sama da mutane 50 a cikin mako biyu.

“Muna matukar jinjina ga jami’an tsaron Najeriya akan kokarin da suke na yaki da ‘yan bindiga, amma dole zamu bayyana cewa lamarinsu na nema ya wuce gona da iri. Bamu san irin kalaman da zamu yi amfani da su ba mu bayyanawa al’umma cewa abin yayi yawa a yankin mu.

“Ina cikin bakin ciki akan abinda yake faruwa yanzu, saboda yawancin mutanen da ‘yan bindigar suka fi damu bama su damu da wata cutar Coronavirus ba.

‘Zai iya yiwuwa ta shiga ko ina a duniya, amma mu banda mu, harin ‘yan bindiga shine ya zama abinda yake damun mu kullum. A cikin mako biyu kacal munyi asarar sama da mutane 50.

“Ina so nayi amfani da wannan damar na bayyanawa hukumar tsaro ta Najeriya cewa mutane sun fara gajiya da jiran gawon shanu, suna neman su fara daukar makamai su tinkari ‘yan bindigar koma me za’ayi ayi.

“Muna iya bakin kokarin mu don mu dakatar da su, kuma muna nuna musu cewa jami’an tsaron mu suna iya bakin kokarinsu wajen kawo karshen lamarin.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here