Mu ba Malamai ba ne, ba kuma fadakarwa muke yi ba – Sarki Ali Nuhu

0
1452

A wata hira da aka yi da jarumi Ali Nuhu a lokacin da ake tsaka da shagulgulan salla, wacce gidan rediyon Express dake Kano suka gayyace shi, jarumin ya amsa tambayoyi da dama a cikin shirin, sai dai tambayoyin da suka fi jan hankali sune:

Daga karshen 2019 har zuwa wannan lokacin akwai wasu fina-finai da kai ke bada umarni, za a ga cewa akwai wasu kebantattun jarumai da kake sanyawa a cikin fina-finanka irinsu Umar M. Sharif, Maryam Yahya, Hassana Mohd da sauransu, wasu mutane na tambayar mai yasa baza ka bawa wasu jaruman dama ba?

Jarumin ya bada amsa kamar haka: “Wato abu daya da na sani shine tunda aka kafa masana’antar Kannywood ba a taba yin wani darakta ba wanda yake tallata jarumai maza da mata kamar ni, idan kuma har za ayi wannan korafin to akwai matsala kenan, domin kuwa akalla mata 12 zuwa 13 na tallata da maza guda 9 zuwa 10 duka ni na tallata su suka zama jarumai.

“Haka kuma akan maganar aiki ya kamata mutane su gane ko a fim din FKD idan ni Ali Nuhu ban dace a wuri ba, ba a saka ni a wannan wuri, kwanan nan na kammala wani sabon fim mai suna ‘Bana Bakwai’ ban fito a ciki. Babu ni a ciki saboda babu inda zan iya taka rawa a ciki.

A karshe an tambayi jarumin wace irin shawara zai bayar domin bunkasa wannan harka ta fim? Sai ya bada amsa da cewa abu na farko shi ne duk wanda yake ganin yana da hanya da zai iya nemo hannun jarin da zai bunkasa wannan masana’anta to yayi, domin kasuwancin fim din shi yafi akan yawan yin fim, in ka yi fim din ina zaka kai?

Kuma wani lokacin za ka ji mutane suna cewa fadakarwa mu keyi, abinda nake so mutane su gane shi ne mai yin fim ba Malami bane mai koyar da tarbiyya, aa shi nishadantarwa yake, amma a cikin wannan nishandatar da kai da yake kana iya samun sakonni na wasu abubuwa na gyaran halayya, amma fa ba Malami bane, za ka ji ana cewa kuna cewa kuna fadakarwa; ni na bude baki na ce muku fadakarwa nake?

Ga wani dan bangare daga cikin shirin da kuma tambayoyi da al’umma suka dinga yi mishi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here