Maza masu gemu sun fi kyau da jan hankalin ‘yammata – Bincike

0
5586

A lokacin baya masu gemu suna zaune cikin rashin jin dadi ne saboda maganganu da habaici da ake yi musu a wancan lokacin, amma a yanzu komai ya canja, a wani bincike da aka gabatar, maza ma su gemu sun fi jan hankali da kyau fiye da wadanda ba su da gemu.

Musulmai suna ajiye gemu ne saboda bin sunna irin ta Ma’aiki (SAW), sannan kuma su cika addininsu. Sai dai kuma gemu ba komai bane a yanzu domin kuwa wadanda ba Musulman ba ma suna ajiye shi.

Binciken ya nuna cewa namijin da ya bar gemu yafi siffar karfi da kyau a idon ‘yammata. Haka kuma binciken ya nuna cewa mazan da suke da gemu anfi saurin amincewa da su fiye da wadanda ba su da shi.

Haka kuma binciken ya bayyana cewa maza masu gemu basa yaudarar yammata. An fi yi musu kallo na kamala. Sun fi ganewa suyi aure fiye da bata lokacinsu wajen neman mata a titi.

Binciken wanda Journal of Evolutionary Biology ya gabatar, ya bukaci mata 8,500 da su zabi tsakanin maza masu gemu da wadanda basu da gemu a matsayin wadanda za su zauna da su matsayin mazajen aure.

An sanya hotunan mazan sahu bisa sahu, inda aka sanya masu dogon gemu, madaidaici, da kuma wadanda babu gemun ma baki daya.

Abin mamaki yawancin matan sun zabi wadanda suke da dogon gemu, sai kuma madaidaici.

Haka binciken ya bayyana dalilin da ya sanya gemu ya zama abin so a wajen mata, inda ya lissafo wasu muhimman abubuwa da gemu yake da su a jikin mutum. Zamu kawo muku su nan ba da dadewa ba.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here