Matsalar tsaro: ‘Yan Sakai ne suke sawa ake kashe mutane a Katsina – Masari

0
361

Sakamakon yawan hare-hare da ake kara samu a jihar Katsina, gwamnatin jihar ta caccaki ‘Yan Sakai, akan cewa sune suke sanyawa ake wannan kashe-kashe a jihar.

A cewar Daily Trust, hakan ya fito daga bakin gwamnan jihar Aminu Bello Masari a jiya Lahadi 28 ga watan Yuni, a lokacin da ya kai ziyara sansanin ‘yan gudun hijira dake karamar hukumar Dandume a jihar.

A yayin da yake zargin cewa abubuwan da ‘Yan Sakai din suke yi yana kawo cikas ga ayyukan jami’an tsaro, Masari yayi gargadi sosai, inda ya ce gwamnatin jihar kawai tana goyon bayan ‘Yan Sakai da hukumomin tsaro suka sani.

Ya ce: “Bamu yadda da wasu ‘Yan Sakai ba, saboda a lokuta da dama, sune suke tsokano ‘yan bindiga suna kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba.”

“Yan Sakai suna iya tafiyar kilomita 30 daga inda suke su kashe Bafulatani, ko kuma duk wani wanda suke zargin dan bindiga ne, kuma a lokacin da ‘yan bindigar suka gani, sai su kai hari kauyen da yake da kusanci da su. Haka ya faru a Kadisau, da kuma kauyuka da dama da aka kashe mutane da yawa.”

A baya dai gwamnatin tarayya tayi zargin cewa Sarakunan gargajiya ne suke taimakawa ‘yan bindigar suke kashe al’umma a Najeriya.

Hakan ya fito daga bakin babban mai taimakawa shugaban kasa a fannin yada labarai, Malam Garba Shehu, sai dai amma bai bayyana sunayen wadanda fadar shugaban kasar take zargi ba.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here