Matsalar tsaro: Ku kara hakuri – Buhari ya roki masu zanga-zanga

0
308

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki mutanen jihar Katsina da su kara, sannan kuma su zama masu goyon baya akan jan aikin da sojoji suke yi a jihar.

A wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata daga bakin mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya nuna damuwarsa akan mutanen da aka yiwa barna ta dukiya, da wadanda suka ji ciwuka da kuma wadanda suka rasa rayukansu akan wannan hare-hare da ‘yan bindga suke kai wa.

Ya ce jami’an tsaron Najeriya a shirye suke su kawo karshen ‘yan bindigar da ta’addanci a Najeriya.

Shugaban kasar yayi gargadin cewa fita yin zanga-zanga akan tituna na iya dauk hankalin jami’an tsaron, inda ya roki mutanen jihar Katsina da kada su fidda rai da kokarin da jami’an tsaro suke yi, wadanda suka kwashe shekaru suna samun nasara akan ‘yan bindigar.

“Manyan dazukan dake arewa maso yammacin Najeriya sun zama gidaje ‘yan bindiga. Harin da za a kai zai tarwatsa wannan dazuka.”

Fadar shugaban kasar ta nemi mutane su kara hakuri, yayin da jami’an tsaro suke daukar matakin da ya dace wajen kawo karshen ‘yan bindigar baki daya.

Shugaba Buhari, wanda ya amince da hada runduna ta hadin guiwa da ta hada da sojoji da ‘yan sanda, wadanda za su kai hari kan ‘yan bindigar dake jihohin Niger, Kaduna, Katsina, Zamfara, da Sokoto, ya sha alwashin kara tabbatar da tsaro ta sanya ido, da kuma sanya jiragen sama da za su dinga gane abinda ke faruwa ko a cikin dare ne.

“Sojojin Najeriya sun nuna bajintarsu a baya, kuma a yanzu ma za su kara yi ta hanyar kawo karshen wannan matsalar,” cewar shugaba Buhari.

A ranar 11 ga watan Yuni ne dai matasa suka rufe babbar hanyar Kankara zuwa Katsina dake kusa da kauyen Yantumaki dake karamar hukumar Danmusa, inda suke zanga-zanga akan matsalar tsaro a yankin.

Daruruwan matafiya sun kasa samun hanyar wucewa, inda suka tsaya a garin Yankara dake karamar hukumar Faskari, saboda rufe hanyar da matasan suka yi bayan harin da aka kai kan al’umma aka kashe sama da mutane 60.

Daily Trust ta ruwaito cewa zanga-zangar ta samo asali ne kwanaki kadan bayan gabatar da wata a kusa da kauyen ‘Yantumaki dake karamar hukumar Danmusa, inda aka jiyo matasa suna wakar fita yaki.

Matasan sun kuma sanya wuta akan babbar hanyar Kankara zuwa Katsina, inda suka hana matafiya wucewa.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here