Matsalar tsaro a Najeriya ta fi yakin basasa da aka yi a baya – Sarkin Daura

0
413

Mai Martaba Sarkin Daura, dake jihar Katsina, Dr Umar Farouk Umar, ya ce halin da Najeriya ke ciki a wannan lokacin na matsalar tsaro yafi halin da ta shiga a lokacin yakin basasa bala’i.

Dr Umar wanda yake shine sarkin garin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito, ya bayyana haka ne a lokacin da shugaban hukumar sojojin Najeriya, Lt. Generak Tukur Buratai, ya kai mi shi ziyara fadar shi.

Sarkin yayi kira da abi hanyar da aka bi a baya wajen kawo karshen yakin basasar don kawo karshen matsalar tsaron a Najeriya.

Yayin da yake bawa Burarai shawara da ya cigaba da dagewa, sannan yayi watsi da maganganun mutane na jan hankali, Sarkin ya yabawa sojojin Najeriya da shugabanninta bisa kokarin da take yi na dakile matsalolin tsaro a Najeriya da jihar Katsina.

Dr Farouk yayi amfani da wannan damar don godewa sojojin Najeriya saboda kafa sansanin soji da suka yi a garin Daura, don kawo karshen matsalar tsaro a yankin da sauran wuraren dake makwabtaka da su.

Ana cigaba da samun matsalar tsaro dai a Najeriya, duk kuwa da cewa hafsosin tsaro sun bayyana cewa za su kare rayukan al’ummar kasar.

A jihar Katsina dai ‘yan bindigar sun kai hari a mahaifar shugaban kasar, inda ya jawo mutane da yawa suka fara gudun hijira daga kauyukansu suna shiga wasu garuruwan yayin da harin yayi kamari a ‘yan makonnin da suka gabata.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin yayi muni da ta kai ga mutanen gari sun fara biyan ‘yan bindiga kudi a kowanne wata don kare kansu daga hare-haren da suke kai wa.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here