Matsalar tattalin arziki: Atiku ya bukaci Buhari ya sayar da jiragen shugaban kasa

0
386

Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewa Najeriya na cikin matsalar tattalin arziki, inda ya bukaci gwamnatin tarayyar ta rage kasafin kudin shekarar 2020 da kashi 25 cikin dari, domin yayi daidai da halin da ake ciki.

A wata sanarwa da ya ofishinsa ya fitar a yau Talata, ya ce ba zai yiwu Najeriya ta cigaba da shiga matsalar tattalin arziki ba, yayin da take cigaba da kashewa jiragen fadar shugaban kasa kudade.

“Ba wai muna cutar da kanmu bane kawai, hatta ‘ya’yanmu da jikokin mu mun sanya su a cikin matsalar bashin da muke ciyowa, wanda su basu ma san da shi ba.

“Saboda haka ina kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki matakin gaggawa wajen rage kudaden da take kashewa, musamman ga abubuwan da basu da amfani, misali kudaden da ake kashewa jiragen fadar shugaban kasa, da kuma gyare-gyaren wurare ga manyan jami’an gwamnati, tafiye-tafiye zuwa kasashen ketare don magani, da kuma naira biliyan 4.6 da ake kashewa fadar shugaban kasa kowacce shekara da sauransu.

“Maganar gaskiya dole Najeriya ta sayar da wadannan jirage ta juya kudaden zuwa wasu abubuwa masu amfani, domin rage kashe kudaden da ake tafiyar da gwamnatin mu.

Atiku wanda ya fito takarar shugaban kasa a zaben da ya gabata na shekarar 2019 a karkashin jam’iyyar PDP, ya Najeriya na cikin wani hali, kuma ba zai yiwu ta cigaba da tafiya ba ta hanyar ciyo bashi da take yi ba a yanzu.

Ya ce: “Ya ce hakan ba wai yana nufin muna ciyo bashi dan cigaban kasa bane, kamar muna satar kudi ne a wajen ‘ya’yanmu, kuma muna jira su biya.”

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here