Matsalar fyade: Hadiza Gabon ta mayarwa da Nazir Sarkin Waka martani akan wani rubutu da yayi

1
808

Kamar yadda kowa ya sani matsalar fyade wata matsala ce da ta dade tana ciwa al’umma tuwo a kwarya ba tun yau ba, an sha kawo labarai da rahotanni kan yadda matsalar ke kara yaduwa a cikin al’umma.

Lamarin ya kai matsayin da ya wuce tsakanin makwabta, malaman makaranta da ‘yan uwa, ya kai matsayin da tsakanin uba da ‘ya’yansa ana samun irin wannan ta’asa, inda takan shafi ‘yan mata, yara kanana, tsofaffi, matan aure har ma da jarirai wadanda basu san komai ba.

A ‘yan kwanakin nan, bayan biyo bayan rahotannin fyade da ke ta kara yawa a Najeriya, ya sanya mutane ke gabatar da wata kwarya-kwaryar zanga-zanga a yanar gizo, inda kowanne mai amfani da shafin yanar gizo ke rubuta jawabi akan nuna rashin goyon bayan wannan mummunar al’ada.

Fitaccen mawaki Nazir M Ahmad, wanda aka fi sani da Sarkin Waka, shima ya kasance daya daga cikin wadanda suka bayyana ra’ayinsu, inda ya wallafa wani rubutu a shafinsa ya ce:

“Karku damu kawai ku rufe tsiraicin ku, tunda Allah ne ya fada. Zaku ga fyade yayi sauki.”

https://www.instagram.com/p/CA_UsaWJ0CY/?utm_source=ig_web_copy_link
Post Source: Nazir M Ahmad Instagram Page

Sai dai wannan rubutu nasa ya tada hazo sosai a yanar gizo, inda mata da wasu daga cikin wadanda suka sabawa fahimtar sa suka fara kalubalantar sa da cewa rubutun nasa ba daidai bane kamar yana goyon bayan masu fyade ne.

Fitacciyar jaruma Hadiza Gabon ma tayi tsokaci a kasan rubutun nasa, inda ta kalubalance shi, duk da cewa daga baya ta goge rubutun nata, amma Tashar Youtube ta Tsakar Gida t samu damar samun kwafin sa, ga abinda ta rubuta:

Bayan ita mutane da dama sun soki wannan lamari na Nazir, inda hakan ya sanya shi yin bidiyon dole dake kara karfafa batunsaa na cewa a Najeriya mutum ne zai gyara ba wai sai mutum ya jira an gyara masa ba.

Video Source: Nazir M Ahmad Instagram Page

Duk da haka dai Nazir bai samu goyon bayan al’umma dari bisa dari ba, hakan ta sanya ya sake wallafa wani bidiyon inda ya ce:

“A kula da yaran ne da nace bai ba ko kuwa a rufe tsiraicin ko addu’ar?”

Post Source: Nazir M Ahmad Instagram Page

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

1 COMMENT

  1. As I Sulaiman the thing that nazir said is true am be in his back mata akulke tsuraici akula da yaya saboda axamaninnan na yanxu xakaga mace tanasa wadansu irin tufafi kayanda gwanda ace batasaba to miyasa maza baxasu rinka jin sha,awar masusa irin wannan tufafin ba Amman inkika kulle ko ina kowa xaiganki cikin mutunci da kamala Dan allh akula Allah ya kyauta

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here